May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotu ta yanke wa dan China hukuncin daurin shekara biyar

1 min read

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin babban birnin jihar Kwara ta yanke wa wani dan China Gang Deng, hukuncin daurin shekara biyar saboda zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

A wani sako da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce an gurfanar da dan Chinan mai shekara 29 kan zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da mallakar ma’aidai masu yawa ba bisa ka’ida ba.

Hukumar ta kama mista Gang a kauyen Tsagari, da ke karamar hukumar Edu a jihar a watan Satumba

Hukumar ta zarge shi da mallakar ma’adinai da nauyinsu ya kai ton 25, wadanda ake fitar da su zuwa kasar China domin yin baturan ababen hawa, da na wayar hannu, da na kyamarori, da kuma wasu na’urori masu amfani da wutar lantarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *