May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ganduje Ya Karkatar Da Dukiyar Gwamnati Don Yakin Neman Zaben Dansa —NNPP

2 min read

Jam’iyyar NNPP ta zargi Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da karkatar da dukiyar gwamnati zuwa yakin neman zaben dansa, Abba, a zaben 2023.

NNPP ta yi zargin mayar da motoci 30 kirar Hilux na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano (KIRS) zuwa na yakin neman zaben Abba Ganduje, wanda ke takarar dan Majalisar Tarayya na Mazabar Tofa/Rimin Gado.

Shugaban NNPP Reshen Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce, “Muna kira ga hukumar EFCC da ICPC su binciki wannan lamari na karkatar da dukiyar al’umma da saba ka’idar aiki da kuma karya dokar zabe.”

Ya yi wannan batu ne yana mai diga alamar tambaya kan dalilin gwamnatin jihar na mayar da wata cibiyar gwamnati wajen ajiye motocin yakin neman zaben Abba Ganduje.

Za mu dauki matakin shari’a —KIRS
Sai dai hukumar KIRS ta karyata zargin tare da barazanar daukar matakin Shari’a kan abin da ta kira kazafin da shugaban NNPP na Jihar Kano ya yi don goga mata kashin kaji.

Sanarwar da kakakin KIRS, Rabi’u Saleh Rimingado ya fitar ta ce motoci 30 da aka gani like da hotunan Abba Ganduje, dan takarar ya tanade su ne domin raba wa shugabannin gunduma na APC a mazabar Tofa/Rimingado da ke goyon bayansa, bayan dan majalisa mai ci, Tijjani Jobe ya raba kananan motoci 20.

Ya ce an ajiye motocin ne a harabar Jam’i’ar Yusuf Maitama Sule, kafin a raba su ga jagororin APC na mazabar da Abba ke neman wakilta.

Zuwa lokacin hada wannan labari dai ba a samu ji ta bankin Abba Ganduje ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *