May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan fashi uku tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

1 min read

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto wasu matafiya da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Kaduna-Zaria a yau Alhamis bayan samun bayanan sirri, inda sojojin suka sha karfin masu garkuwa da mutanen bayan daukar sa’o’i ana ɓata kashi.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun ƙakakinta, Onyema Nwachukwu, ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda guda biyu a wasu samame da ta kai Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya a ƙauyen Abasia-Amale da ke karamar hukumar Ɓirnin Gwari na Jihar Kaduna a jiya Laraba.

Ɓirgediya Onyema ya kuma bayyana cewa sojojin sun ƙwato ɓindigar AK-47 da harsasai da kuma wayoyin salula a hannun ‘yan ta’addan.

Wasu rahotanni kuma na cewa a safiyar yau Alhamis ne ‘yan ɓindiga suka toshe hanyar Kaduna zuwa Zaria, inda suka yi ta ɓude wuta kan matafiya da garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba.

Sai dai, sojoji sun mayar da martani nan take ta hanyar fatattakar ‘yan bindigar wanda haka ne ya sanya suka sake wasu matafiya ɓiyar da suka kama tun da farko.

Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya yabawa dakarun saboda jajircewa da suke yi wajen ganin sun kawo ƙarshen ayyukan ‘yan ta’adda a yankin arewa maso yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *