July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ukraine ta zargi Rasha da dasa nakiya a madatsar ruwa

1 min read

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da dasa nakiyoyi a wata madatsar ruwa da ke yankin Kherson a kudancin kasar wadda ke karkashin ikon sojojin Rashar.

Shugaban ya ce idan har aka lalata cibiyar samar da wutar lantarkin ta Kakhhovka, za su shiga cikin bala’i.

Mista Zelensky ya kara da cewa bayanan da suka samu, madatsar ruwan ta Kakhhovka, mamaye take da nakiyoyin da wadanda ya kira ‘yan ta’addar Rasha suka dasa.

Sannan kuma ya ce dubban mutane ne da ke kewayen kogin Dnipro za su kasance cikin hadarin ambaliya.

Shugaba Zelensky ya fada wa taron shugabannin Turai a Brussels cewa Rasha na son bayar da damar a mayar da wuraren makamashi a matsayin fagen daga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *