May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Budaddiyar Wasika Zuwa ga Mai Girma Gwamna-Khadimul Islam Tare da girmamawa da fatan alkhairi ga mai girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, OFR, Khadimul Islam

4 min read

Na rubuta wannan wasika ne domin na isar da wani muhimmin sako ga mai girma gwamna da `yan majalisar sa da sauran wadan da abun ya shafa.

Mai Girma Gwamna, na tabbata ka na sane da cewa ana lissafa Jihar Kano a matsayin gari mai dunbin tarihi tare da kulawa da alamuran addini da inganta shi da kuma malamai masana Allah da manzon sa sallahu alaihi wasallam. Wannan ya sanya baa taba barin mu a baya ba a al`amarin addini da rayuwa. Wannan ya sanya bayan farfado da shariar musulinci a shekara ta 2000 Kano ta na daya daga cikin Jihohin da suka yi wuf suka amshi abinda sun san na su ne. A wannan lokaci abinda ya sa aka samu gagarumin karba ga wannan tsari shine tabbaci da Musulmai suke da shi cewa idan aka aiwatar da wannnan tsarin zai basu makoma mai kyau anan duniya da ranar gobe kiyama.

Alhamdulillahi, sakamakon haka aka kafa hukumomi da kotuna da cibiyoyi domin fara aiwatar da wannan gagarumin tsari. Wannan sun hada hukumar zakka da hubusi, da kuma hukamar sharia da kuma hukumar adaidaita sahu da kuma hukumar hisba da kuma kotuna na shariar musulinci da alkalai masana wannan tsari da ofishin mai bada shawara a harkar addini da dai sauran su. Haka kuma mafi yawan hukumomin gwamnati sun kasance suna sa ka mizani na sharia a aiyukan su da abubuwa makamantan haka. Haka kuma aka zauna akayi gyara ga penal codes aka samar da sharia penal codes da zaa dinga amfani da su a duk lokacin da sharia zuwa ga alkali ta tashi.

A unguwanni kuwa suma jama`a baa bar su a baya ba domin an kafa kwamitoci na zauren sulhu wadanda har yanzu wasu suna ci gaba da aikin da ya kamata. Abinda mutane suke da yakini shine idan akayi amfani da wannan tsari zai kawo ci gaba mai dorewa, zai rage cin hanci da rashawa a cikin al`uma, zai rage sace sace na dukiyoyin al`uma a gwamnata ce da kuma a cikin aluma, zai rage aikin masha`a a cikin al`uma kamar su zinace-zinace da shan giya, zai samar da aiyukan yi domin adalci zai tabbata, zai rage talauci ta hanyar inganta hanyar samun halak da bayar da zakka da kula da marayu da gina dan adam da dai makamatan su. Sannan babban abun zai kawo yardar Allah da warakar al`amura cikin al`uma. Hakika an samu nasarori a wasu bangarorin a gwamnatocin da suka gabata kamar harkar kula da marayu da harkar zakka da kuma inganta rayuwar dan adam.

Mai girma Gwamna hakika dole a yabawa hukumar hisba a karkashin jagorancin ka da kafin ka, domin suna fitar da sakamakon da shi ya sa aka kafa wannan hukuma duk da cewa akwai matsaloli da suke bukatar a kara duba su.

Mai girma gwamna, abinda ya ja hankali na na yi wannan rubutu shine jihar Kano, yanzu tana cikin jihohi da talauci yayiwa katutu a Najeriya. Barace barace a masallatai da unguwanni da gidajen watsa labarai ya zama ruwan dare. A lokaci guda kuma ga hukuma da aka kafa domin karbar hakkin Allah daga hannun mawadata domin a maida shi zuwa ga talakawa kamar yadda ya zo a cikin suratu Tauba aya ta 103.

Abin tambaya shin gwamnati ta bawa wannan hukuma kulawa ko kuwa dai kawai jeka na yi ka ne? Misali, a farkon wannan shekarar kowa ya sani gwamnati ta dauki maaikatan karbar haraji sama da 600 a jahar Kano. Wannan ci gaba ne domin ya samawa matasa aiyukan yi, amma mutum nawa aka dauka domin aikin tattara zakka da rabata?

Mai Girma Gwamna, hakikanin gaskiya Jihar Kano ta huce matsayin da ta samu kanta a harkar zakka domin kuwa mun san me ake yi a wasu kasashe da kuma makotan jihohi ma a Najeria. Misali, Masarautar Dutse kadai ta na tattara zakkar da Kano ba ta hadawa a Shekara? Me wannan yake nunawa? Haka wannan abin yake a Kazaure, Hadejia da sauran makota. Wasu kasashen kuwa tuni sunyi amfani da ita sun kawar da talauci da rashin aiyukan yi, saboda haka muma za mu iya.

Mai girma Gwamna, wannan tunatarwa ce kuma fata na shine tazo gare ka domin wata kila ragowar lokacin da Allah ya baka za ka iya amfani da shi domin inganta harkar zakka da rage talauci da bara ce barace a wannan gari mai albarka. Ina ba da shawarar a shigo da masarautu cikin harkannan a kuma yi hadin gwiwa da duk wani mai fada a ji a Jiha.

A karshe ina mai yaba maka da kulawa da harkar tsaro da ka ke da kuma fatan Allah ya ci gaba da tsare alumar jihar Kano da musulmi baki daya ya kuma yi muku jagora domin sauke nauyin da Allah ya dora muku.
Wassalam.

Aliyu Dahiru Muhammad, PhD.
Department of Economics
Bayero University Kano.
[email protected]
21/10/2022

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *