May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Direbobin Manyan Motoci Sun Toshe Babbar Hanyar Benin

1 min read

Daruruwan direbobin manyan motocin daukar kaya ne suka toshe babbar hanyar Auchi zuwa Benin domin nuna fushinsu kan lalalcewar hanyar.

Direbobin dauke da kwalayen da aka yi rubuce-rubuce, sun rufe mahadar hanyar Ajatu da ke Karamar Hukumar Etsako ta Yamma ta jihar, wanda hakan ya hana ababen hawa wucewa.

,Hakan ya haddasa cinkoson ababen hawa mai muni, inda jerin gwanon motoci daga wurin ya kai tsawon kilomita biyu daga kowanne bangare.

Mista Donald Etamob da ke magana da yawun direbobin ya ce, ba za su bude hanyar ba, har sai Gwamnatin Tarayya ta biya musu bukatunsu.

Shugaban masu zanga-zangar ya ce hakan ya zama dole saboda yadda hanyar ta lalalace, da kuma yadda rashin daukar matakin da ya kamata daga hukumomin da abin da ya shafa.

Ya kuma ce daya hanyar da suke bi su wuce zuwa Benin, Gwamnatin Jihar Edo ta toshe ta.

Wani da wanda cinkoson ya rutsa da shi ya fada wa wakilinmu cewa, ya kwashe awanni tsaye a wuri daya, yayin da tafiyar minto 30 zuwa Benin daga nan, ta zama tafiyar yini guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *