May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 603 a Najeriya, miliyan ɗaya sun rasa gidajensu

1 min read

Ma’aikatar jin kai ta Najeriya ta fitar da sabbin alkaluman na yawan adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar.

Ministar ma’aikatar Sadiya Farouk, ta ce yawan mutanen sun kai 603.

Sannan kuma an kiyasta cewa mutane fiye da miliyan daya da dubu 300 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliya ruwa a fadin kasar.

Ministar ta ce: ”Akwai wadanda suka ji raunuka sakamakon ambaliyar wanda yawansu ya kai 2,407,, sannan kuma akwai gidaje dubu 121, 318 da ambaliyar ta shafa.”

Sadiya Farouk, ta ce akwai kuma gidaje fiye da 82,000 da suka rushe gaba ɗaya.

Ministar ta ƙara da cewa sakamakon abin da ya faru a bana, akwai matakan da ya kamata a dauka na kauce wa samun irin wannan mummunar asara, kamar kwashe mutanen da ke zaune a yankunan da ke gabar ruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *