May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An buɗe ƙananan hukumomin da aka rufe a Zamfara

1 min read

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince ta sake bude kananan hukumomin Gummi da Anka da kuma Bukkuyum wadanda ta rufe saboda dalilai na tsaro.

Sanawar da kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara ya sanyawa hannu ta ce umurnin budewar ta shafi kasuwanni da manyan hanyoyi a kananan hukumomin jihar.

Sai dai sanarwar ta bukaci jama’a su kasance masu bin doka da oda.

A makon da ya wuce ne gwamnatin Bello Mohammed ta sanar da rufe kananan hukumomin domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *