May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shirya taron Maulidi dan tunawa da Ranar Haihuwar Annabi Muhammad S.A.W jawabi ne-Malam Hussain Ilyasu

1 min read

Wani Malamin Andinin Musulunci a nan Kano Malam Hussain Ilyasu Dambare ya bukaci al’umma dasu fito su zabi shugabanni nagari wanda zasu kawowa kasar nan cigaba.

Malamin Hussain yayi wannan kira ne yayin bikin taron Maulidin Annabi Muhammad S.A.W wanda ya gudana a unguwar ta Dambare.

Malamin ya kuma ce ganin irin halin da al’umma suka tsinci kansu na matsalin rayuwa akwai bukatar zabar shugabanni nagari.

Ya Kara da cewa sun shirya taron ne da nufin tunawa da murnar Ranar da aka haifi Annabi Muhammmad S.A.W wanda aka saba gudanarwa a Madinatu Danbare.

Malamin ya kuma ce jawabi ne al’umma musulmi su cigaba da yada tarihin Annabi Muhammad S.A.W da a halinsa baki daya.


Da suke gabatar da jawabi Sharu Mustapha kasim Sani Mainage da sharu Ibrahim suna cikin mahalarta taron sun bayyana farin cikin a bisa gudanar da taron inda sika bayyana kira ga al’umma muhimmancin kare janibin Annabi Muhammad S.A.W da a halinsa.

A yayin taron dai a’lumma da dama ne suka halarta inda aka gabatar da karatuttuka da kasidu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *