July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

EFCC ta sake gurfanar da tsohon akanta janar Ahmad Idris

2 min read

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC ta sake gurfanar da tsohon akanta janar din kasar Ahmad Idris da wasu mutum 3 a gaban wata bababr kotun da ke Abuja kan zargin sama da fadi da kusan naira billiyan 109.

Saura mutum uku sun hada da Olusegun Akindele da Muhamamd Usman da Gezawa Commodity and Exchange limited.

An dai fara gurfanar da wadan da ake zargi a gaban kotun mai shari’a Adeyemi Ajayi a cikin watan Yulin da ya gabata, bisa zargin laifuka 13 da ke da alaƙa da almubazarancin naira biliyan 109, wanda daga bisani aka mayar da shari’ar gaban mai shari’a Yusuf Halilu.

A yayin zama kotun na yau, wadanda ake zargi sun musanta laifukansu.

Hukumar EFCC ta dai yi zargin cewar a tsakanin watan Fabareru zuwa watan Decembar 2021, tsohon akanta janar din, Ahmad Idris ya karbi cin hanci na naira biliyan 15 da miliyan 1 daga hannun Olusegun Akindele, a matsayin karin ƙaimi wajen hanzarata amincewa da biyan kashi 13 ga jihohin 9 na Najeriya da ke da arzikin man fetur, da za a yi ta karkashin ofishin babban akanta janar na kasa.

Haka zalika EFCC ɗin ta kuma zargi Olusegun Akindele da Muhamamd Usman, da karkatar da kimanin naira biliyan 84 daga asusun gwamnatin tarayya, a tsakanin watanin Fabarairu zuwa Nuwamban 2021.

Hukumar EFCC ɗin dai ta ce laifin ya ci karo da sashen 155 da na 315 na kundin manyan laifuka na Penal Code, ta Najeriya na 1990.

Yanzu dai mai shari’a Yusuf halilu ya dage ci gaba da zaman kotun zuwa ranar 23 ga watan Nuwambar 2022, don kara saurararon shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *