May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan sandan Jihar Sokoto sun kama mutum ɗauke da katin zaɓe 101

1 min read

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya reshen Jihar Sokoto ta yi kira ga mazauna jihar da su je su duba katikan zaɓensu bayan ta kama wani mutum ɗauke da katin zaɓe 101.

Kakakin ‘yan sandan jihar ya faɗa wa BBC Hausa cewa kwamashinan ‘yan sanda ne ya gabatar da Ahassan Idris bayan sun kama shi a yankin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.

A baya-bayan nan akan kama mutane da ɗumbin katin zaɓe da ake zargin ‘yan siyasa ne masu yunƙurin amfani da su don yin maguɗin zaɓe watanni ƙalilan kafin babban zaɓen ƙasar na 2023.

DSP Sanusi Abubakar ya yi wa Umaymah Sani Abdulmumin ƙarin bayani a wannan sautin da ke ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *