May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ko yi da halayan Annabi Muhammad S.A.W shi abu mafi Muhimmanci ga Al’ummar musulmi.-Malam Askia Shekih Muhammad Nasir Kabara

1 min read

An bukaci al’umma dasu ringa shirya tarukan fadakar da al’umma kan irin matsayin da Annabi Muhammad S.A.W yake dashi tare da fito da irin matsayi da gudunmawar da sahabban Annabi Muhammad S.A.W suka baiwa Addinin Musulunci.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin daya daga cikin jagororin gamayyar kungiyoyin taimakon Al’umma ta kasa da hadin gwiwar Kungiyar Iddef wanda Malam Dakta Askia Dakta Sheikh Muhammad Nasir Kabara, a yayin taron Walimar Mauludin Annabi Muhammad S.A.W wanda ya gudana a jiya.

Dakta Askia ya kuma ce,babban abin Shi ne hadin kan al’ummar Annabi Muhammad S.A.W wanda gashi an hadu guri guda an gudanar da walimar cin abinci cikin farin ciki kowa yana murna da haduwa da sauran al’umma masoya Annabi Muhammad.

Ya kuma bukaci al’umma dasu hada kansu waje guda dan ganin sun yaki kokarin wanda ba musulmi ba, na ganin sun raba kan yan uwa musulmi.

Ya Kara da cewa dole sai musulmi sun ajjiye banbancin Addini sun tsaya tsintsiya madaurinki daya sannan za’a sami nasara.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana farin cikin su bisa gudanar da taron Walimar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *