May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Matsalar tsaron da ta fi damun matasa a Kano

3 min read

A bayyana take cewa matsalolin tsaro sun addabi kowane lungu da saƙo na Najeriya, amma kowane yanki da nau’in matsalar da ta fi damun su a ɓangaremn tsaron.

Ga mazauna birnin Kano da kewaye, matsalar daba da haura wa gidajen mutane don yin sata da kwararar ‘yan gudun hijira.

Wannan dalili ya sa gwamnatin jihar ta saka dokar hana zirga-zirgar babura masu ƙafa uku na haya daga ƙarfe 10:00 na dare

Wasu matasa uku sun faɗa wa BBC Hausa labaransu na irin halin da suka shiga sakamakon matsalolin tsaron da suka ritsa da su.

‘Yanzu suna zuwa caka maka wuƙa za su yi’
Wata matsala da ta yi yi ƙamari a baya-bayan nan a ƙwaryar birni ita ce ta ƙwacen waya.

Matashi Aliyu Doguwa mai shekara 22 ya taɓa faɗa wa hannunsu. Duk da cewa ya tsira ba tare da ya sha sara ko suka ba, wani abokinsa bai yi sa’a ba a farkon shekarar 2022.

“Akwai abokina a nan (unguwar) Yahaya Gusau, suna zuwa kawai yankarsa suka fara yi da wuƙa,” in ji shi, “sai da aka kai shi asibiti ma ya yi jinya.”

Aliyu ya ce yanzu ‘yan daba “har alfahari suke yi da adadin mutanen da suka kashe kuma yanzu da sun zo kawai caka maka wuƙa za su yi”.

Game da abin da ya faru da shi kansa Aliyu kuwa, ya ce lokacin da suka tare shi a kan Titin Gidan Gwamnati (State Road) shi kan sa bai san abubuwan da ya ba su ba.

“Suna tare ni kawai na ɗauki abin da yake jikina na ba su ba tare da wata gardama ba, ni ban san ma abin da na ba su ba,” in ji matashin mazaunin unguwar Sharaɗa.

Matashin wanda ɗalibi ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya ƙara da cewa sai daga baya ya gane cewa wayarsa ya miƙa musu da kuma kuɗi naira 5,000.

Ko wane mataki Aliyu ya ɗauka game da lamarin? “Banki na je na yi musu ƙorafi kuma suka ba ni wasu fom-fom na cike, na sauya layin da na yi rajista da shi…tun da na yi musu ƙorafi su sun san abin da za su yi.”

‘Sau uku ana sace min waya a ɗakinmu’
Yusuf Umar matashi ne mai shekara 25, wanda ke karatu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil.

Ya faɗa wa BBC cewa sau uku ana sace masa waya a karo uku daban-daban, kodayeka ya ce daga baya ya samu madadinsu masu yawa.

“Kuna cikin ɗaki a kwance sai a shiga a ɗebe muku wayoyi,” in ji matashin mazaunin unguwar Makwalla Ƙofar Yamma da ke garin Wudil a wajen birnin Kano.

“An ɗauke min waya kamar sau huɗu kuma duka a ɗaki ɗaya, amma maganar da ke ma yanzu na bar ɗakin.”

Yusuf ya ƙara da cewa an taɓa haura wa gidan yayansa mai suna Kabiru Sani kuma aka ɗauke masa babur.

Matashin ya fara yin waya a shekarar 2014, wadda mahaifinsa ya ba shi amma da wuya in an shekara wani ɗan-acaɓa ya raba shi da ita.

“Faɗuwa ta yi wani (ɗan-acaɓa) ya tsinta, sai ya zo yana cigiya kuma aka faɗa masa tawa ce. Daga baya da aka sake tuntuɓarsa sai ya ce ya bar Kano.

“Ta biyun kuma, na gama ninke kayana na ajiye, ina dubawa sai na ga babu waya.

“Ta ukun kuma, ita ma muna kwance a ɗaki haka sai kawai na nemi waya na rasa. Ba a ɗauki ta kowa ba sai tawa.”

To, ko malam Yusuf ya sake yin wata wayar bayan waɗan nan? “Alhamdulillahi a yanzu Allah ya mayar min da alkairinsu da yawa,” a cewarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *