May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abin da ya jawo faɗa tsakanin Murtala Garo da Ado Doguwa

3 min read

Ga alama sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC a jihar Kano bayan da taƙaddama ta ɓarke tsakanin ƴaƴan jam’iyyar.

Yayin wani taron jam’iyyar APC a gidan mataimakin gwamnan jihar Kano a ranar Litinin, an samu hayaniyar da ta haifar da nuna yatsa tsakanin Honorabul Alhassan Ado Doguwa da kuma Murtala Sule Garo.

Sa’insa da ka-ce-na-cen ta ɓarke ne lokacin da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Najeriya Honorabul Doguwa ya je gidan mataimakin gwamnan Kano a ranar Litinin.

Hon Doguwa ya shaida wa BBC cewa ko da ya isa wurin sai ya tarar ana wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Kuma a cewarsa da ya tambayi abin da yasa ba a gayyace su ba, sai ya ce an mayar masa da kakkausar amsa.

“Tambayar kawai da na yi ita ce, ‘yanzu ya mai girma mataimakin gwamna ya kamata a ce ana taro irin wannan, ga ɓangaren gwamnati ga kwamishinoni ga ɓangaren majalisar jiha, amma mu da muke majalisar tarayya ba a gayyaci kowa daga cikinmu ba, laifin me muka yi?

“Daga faɗar hakan sai kawai yaron nan Murtala yana zaune ya ce ba za a gayyace ku ɗin ba. Waɗannan kalmomi su suka hassala ni.

“A wajen taron kuma a garin yana masifa yana zagina sai ya kifar da wani kofin shayi mai ruwa a ciki, sai santsi ya kwashe shi ya faɗi ya fasa bakinsa.

“Amma sai na ji ana ta yaɗa wani zance wan na jefe shi na ji masa rauni,” in ji Doguwa.

Tona asirin rikicin siyasar APC a Kano
Wannan dambarwa dai ta fito da wataƙila ɓoyayyiyar matsalar da APC a Kano ke fama da ita, inda Honorabul Doguwa ke ganin ya kamata gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya saka baki tun da babban zaɓe ake fuskanta.

Honorabul Doguwa ya ce “Ai ɓaraka ba za ta ɗinku ba sai idan mai girma gwamna ya yarda cewa kowa ɗansa ne. Sai idan ya yarda yadda Murtala yake ɗansa muma ƴaƴa ne, saboda muna fuskantar muguwar barazana daga ƴan hamayya.

“Kowa ya san tasirin da Kwankwaso yake da shi a jihar Kano, to wannan rigimar kawai ta ishe mu,” ya ce.

Sai dai a nasa bangaren dan takarar mataimakin gwamna a APC Murtala Sule Garo, ya ce lokacin da suke tsaka da taro sai Honorubal Doguwa ya shigo wurin yana wasu maganganu.

“Abin da ya fara cewa tun da abin jin daɗi ake yi na raba kuɗaɗe shi ne ba a neme su ba, idan da abin wahala ne sai a neme shi.

“Mataimakin gwamna da kansa ya ce masa mu ba rabon kudi muke yi ba. Mu da ka ganmu a nan a ce maganar rabon kuɗi ce ta tara mu, wa zai ba mu kuɗin?

“Sai ya ce to me ya sa ba a kira shi taron ba a matsayin kujerarsa. Sai mataimakin gwamna ya ce Gwamna Ganduje ne ya gayyato mutanen.

“Ni ban tanka masa ba ma saboda da mataimakin gwamna yake.

Murtala Sule Garo ya ce ya shiga maganar ne lokacin da Honorabul Doguwa ya zarge shi da cire fastocinsa.

“An sa hotunansa an cire amma da kansa ya ce ya san ba ni ne ba amma na kusa da ni ne suka yi hakan. Sai na ce ba haka aka yi ba.

“Daga fadar hakan sai ya ɗauki kofin da mataimakin gwamna ke shan shayi ya wurga min shi,” in ji Garo.

Sai dai ya ce komai na rayuwa ɗan haƙuri ne.

Har zuwa lokacin rubuta wannan labari dai jam’iyyar APC a Kano ko wani daga cikin gaggan jam’iyyar ba su ce uffan ba, kan wannan yamutsi.

Amma masu lura da al’amuran siyasa na ganin muddin ba a shiga tsakani tare da yi wa tufka hanci ba to akwai yiwuwar su fuskanci cikas.

Kuma a gefe guda jam’iyyun adawa sun zuba ido suna lura da yadda rikicin zai kaya, wataƙila su sami wata gaɓa da za su yi amfani da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *