July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotu Ta Sa Ranar Yanke Hukunci Kan Karar Da Aka Shigar Da Hadiza Gabon

1 min read

Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari, a Jihar Kaduna ta sa ranar 15 ga watan Nuwamban 2022 don zartar da hukunci a karar da aka shigar da fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon.

Aminiya ta rawaito wani Bala Musa, ma’aikacin gwamnati ya kai karar jarumar bisa zargin kin aurensa bayan ya kashe mata kudin da suka kai har Naira dubu 396.
Bala dai ya ce sun yi soyayya da jarumar kuma ta yi alkawarin aurensa.

Gabon dai ta musanta saninsa, inda ta ce ba ta taba haduwa da shi ba a rayuwarta.

A ranar Laraba ce Alkalin kotun, Mai Shari’a Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage sauraren karar bayan wani babban lauya, Sulaiman Lere, ya roki kotu da ta ba shi dama ya tattauna da bangarorin biyu domin sasanta lamarin.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Barista Nurudeen Murtala, ya goyi bayan shawarar sasantawa da Barista Lere ya yi, inda ya kara da cewa sulhu abu ne da Allah yake so, don haka ba za a yi adawa da shi ba.

A nasa bangaren, lauyan wanda ake tuhuma Barista Mubarak Sani, ya goyi bayan shawarar sasantawa amma ya roki kotun da ta saurari shaidun da ya gabatar kan wanda ya shigar da karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *