May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

ASUU na shirin komawa yajin aiki

3 min read

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU na shirin sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta na biya musu bukatunsu.

A wata tattaunawa da mataimakin shugaban kungiyar da BBC ta yi, Dr Chris Piwuna, ya ce kungiyar na shirin gudanar da taron gaggawa domin yanke shawara a kan matakin da za ta dauka a cikin kwanakin nan.

‘’Za mu hadu nan gaba mambobinmu suna mana tambayoyi dole mu hadu mu san amsar da za mu ba su,’’ in ji shi.

Malaman na korafi kan yadda suka ce gwamnati ba ta biya su albashin wata takwas da suka yi suna yajin aiki ba.

Ya ce babu ko daya daga cikin alkawuran da suka yi da gwmnati ta cika.

‘’Ba su rubuta wasika sun ce sun kara mana albashinmu ba yadda muka bukaci su yi,’’ in ji shi.
Amma game da kudin bunkasa jami’o’i ya ce gwamnati ta ce za ta sa a kasafin kudi, kuma Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ‘’ya nuna mana shedar yana cikin budget (kasafin kudi).’’

Abin da mataimakin shugaban ya ce yana daga cikin yarjejeniyar da aka yi da su da Shugaban Majalisar Wakilan wanda ya shiga tsakani a baya.

Dakta Piwuna ya ce albashin kwana 18 kawai gwamnati ta ba su, saboda haka kwanakin da ta biya su sun kare don haka za su dauki mataki.

Dangane da cewa ko za su daina zuwa aiki ne, Kwamared Piwuna ya ce, ‘’ idan mun iya zuwa kan za mu zo. Ka san dai wahalar da ake ciki a kasar nan, kudin mai kudin abinci komai ya tashi.

Ya kara da cewa, ‘’Sai ka samo mai motarka sai ka ci abinci ka samu hankalinka kamun ka zo aiki.’’

Ya yi gargadin cewa, ‘’Zuwan aiki daban yin aiki daban. Za ka iya zuwa aiki ba ka yi aikin ba kuma za ka iya zuwa ba ka yi aikin ba.’’

Malamin jami’ar ya ce tun da farko sun koma bakin aikin ne saboda umarnin kotu da kuma kiran da Gbajabiamila ya yi musu.

‘’Kungiyarmu ba ta amfani da ka ce za ka yi abu kaza. Za ka sa a rubuce ne ga bin da za ka yi idan gobe ba ka yi ba za mu nuna maka takardar da ka sa hannu.’’

‘’To amma yanzu abin bai kai mu yi haka ba. Saboda kotu ta bukaci mu koma kafin kwankin da suka ba mu su wuce,’’ in ji shi.

Ya ce sun gode wa Kakakin Majalisar saboda kokarin da ya yi wajen shiga tsakani, sannan kuma ya ce sun girmama shugabn kasa a kan maganar, ‘’amma yanzu an koma gidan jiya.’’

Kafin kungiyar ta koma bakin aikin na kwanan nan sai da Kotun kolin kasar ta umarce ta ta janye, kafin ta saurari karar da ta gabatar a gabanta, inda kungiyar ta sanar da komawa aikin daga ranar 14 ga watan Oktoba 2022.

Wannan kuwa ya kasance ne bayan kungiyar ta shafe wata takwas tana yajin aiki, wanda ta fara tun daga ranar 14 ga watan Fabrairu na wannan shekara 2022, saboda gwamnati ta ki cika musu alkawuran da suka yi a baya kan bukatunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *