May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An sako ‘yan ƙwadago 21 da aka yi garkuwa da su a Katsina

1 min read

Matasan nan fiye da 20 da aka sace a wata gona a Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Asabar cewa mutum 21 aka sace kuma sun kuɓuta.

“Cikin murna, ina sanar da ku cewa dukkan ma’aikata 21 da aka yi garkuwa da su yayin da suke aiki a wata gona da ke ƙauyen Kamfanin Mailafiya sun kuɓuta,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “an haɗa su da iyayensu kuma ana ci gaba da bincike”. Sai dai bai bayyana ko an biya kuɗin fansa ba kafin sakin nasu.

Tun farko, kafar yaɗa labarai ta Daily Trust ta ruwaito cewa yaran 39 ne aka sace, waɗanda ba su kai shekara 20 ba, kafin shida daga ciki su yi nasarar tserewa daga hannun ‘yan bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *