May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan jarida na da rawar da zasu taka wajen kawo sauyi a bangarori da dama

3 min read

Gidan Radiyon Arewa dake jahar Kano ya shirya wani taro mai ta ken Nijeriya ina mafita karo na biyu a ranar Lahadi 6 ga watan Nuwamba 2022.

Shugaban tashar Arewa Radio Alhaji Shehu Bala Kabara, ya bayyana maƙasudin gudanar da taron da cewa an shirya shi ne ,domin wayar da kan al’umma akan abin da ya shafi siyasa da kuma yadda Yakamata al’umma sun yi duba na tsanaki wajen zaɓen shugabannin da Yakamata domin shawo kan irin matsalolin ake fuskanta a shugabanci da siyasa.

Shehu Bala Kabara ya ƙara da cewa abinda su ke so a cimma bayan wannan taro shi ne kowa ya yi karatun ta nutsa , ya duba ya tsefe ya zaɓi shugaban da Yakamata ta zaɓa duba da irin matsalolin da ake ciki .
Na farko za mu iya cewa haƙƙi ne akan mu , mu kafafan yaɗa labarai da duk ma wata cibiya da take rajin ganin ci gaban al’umma ta kowacce fuska dan al’uma su tsira daga matsalolin da suke ciki.

” Wannan yana ɗaya daga ciki tunda muka ga zaɓe ya ƙara to yakamata mu shirya taro kuma duk shekara mu yi irin wannan taro mu kuma duba ainihin matsalolin da al’umma suke ciki a wannan lokaci dan mu gayyato masana a tattauna akan matsalolin dan samar da mafita.

A ƙarshe Shehu Bala Kabara ya ce ” saƙon da suke fatan ya isa ga al’umma domin wayar mu su kai da kuma su tsaya su yi karatun ta nitsa akan mahadarar da aka yi da abinda ake so a cimma da cewa kowa yaje ya karkaɗe kuri’ar sa amma banda siyasar kuɗi,Ƴan uwantaka da siyasar abokan taka .

Abinda ya kamata mutum ya yi shi ne abinda waɗannan Malamai suka tattauna akai da kuma menene yakamata kayi a matsayin ka na mai bin shugabanni sannan su kuma me ne ne haƙƙin talakawa akansu .

Domin shugaba adali shi ne a duba halayensa mutum ne mai gaskiya da riƙon amana wanda yasan Yakamata.

Na biyu kuma a duba mai mutum ya yi a baya idan ya taɓa riƙe wani muƙami sai aga yaya ya gudanar da wannan abin, idan kuma bai taɓa riƙewa ba to sai a yi la’akari da wannan halaye nasa .

Idan kuma mutum ne da sai da ya yi banga ya ci mutuncin mutane duk waɗannan abubuwa ne da bai kamata a zaɓi mutum ba.

Mallam Lawan Abubakar limamin masallacin juma’a na Triumph ya gabatar da maƙalarsa akan haƙƙin shugabanni akan mabiya da haƙƙoƙin mabiyan akansu ,kuma haƙƙoƙinnan suna da matukar muhimmanci domin rashin sanin su da kuma kiyaye su shi yake kawo Gurɓacewar al’amuran ta ɓangaren su shugabanni ko ta ɓangaren mabiya.

” Daman duk inda kaji ana fitina a duniya daman to kodai ba a san haƙƙi ba ko kuma an sanshi an take shi.
Mallam Lawan Abubakar limamin masallacin juma’a na Triumph ya gabatar da maƙalarsa akan haƙƙin shugabanni akan mabiya da haƙƙoƙin mabiyan akansu ,kuma haƙƙoƙinnan suna da matukar muhimmanci domin rashin sanin su da kuma kiyaye su shi yake kawo Gurɓacewar al’amuran ta ɓangaren su shugabanni ko ta ɓangaren mabiya.

” Daman duk inda kaji ana fitina a duniya daman to kodai ba a san haƙƙi ba ko kuma an sanshi an take shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *