May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu Manoma dake Garin Nata’ala dake karamar hukumar Tudun Wada sun zargi Yan Da’awa da kunno rikici a yankin

2 min read

Manoma a karamar hukumar Tudun Wada sun yi kira ga yan Da’awa dasu guji kunno rikici a yankin domin kauda fitina tsakanin hakimi da talakawansa.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin manoman sun bayyana cewa ‘yan Da’awa sun shiga yankin, inda suka haifar da sabani a tsakanin Hakimi da wasu manoma a garin Na’atala kan maganar gonaki.

A cewar mutanan zargin da ake na cewa hakimi na kwace gonakin al’ummar wannan zance ne, kawai domin batawa hakimin suna suke yi.

Wani Manomi wanda ya nemi a boye sunansa ya shaidawa waikiliyar Hassana Baba Ahmad cewa wasu mutane ne suka dauki nauyin Yan Da’awa suna yada labarin karya tare da kunna rikici tsakanin al’ummar garin.

Ko da wakiliyar mu ta tuntubi Hakimin ya shaida mata cewa gonaki sha biyar da ake magana tuni ma’aikatar kananan hukumomi ta amince dasu kamar yadda takardun mallaka suka tabbatar, wanda hakimin ya bamu domin mu duba kuma mun tabbatar da hakan.

Haka kuma Ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wadannan gonaki suna karkashin Masauratar mu wanda muka gada.

A wata hira da a kayi da shugaban kungiyar Da’awa a jiya game da zargin da akai na cewa wasu mutane na daukar nauyin su suna kunno riki, shugaban ya ce wannan zance ba haka yake ba.

Haka kuma an kuma tambayeshi game da zargin daukar nauyin Yan Jarida domin bata sunan hakimi nan ma ya musanta zargin.

Da aka tambayeshi ko sun ji tabakin hakimin game da zargin cewa ya cinye gonaki, sai ya ce, aa amma suna baiwa hakimi hakuri game da hakan.

Haka zalika an kuma ji tabakinsa cewa ko yan da’adawa sun je ma’aikatar kananan hukumomi game da maganar da hakimi yayi na cewa gonakin suna shaida daga Ma’aikar, a nan ma dai ya ce, aaa basu je ba.

A karshe dai shugaban kungiyar Da’awa ya fito fili ya nemi a fuwar Hakimi bisa wannan labarai da aka yada a radio da kuma wasu daga cikin shafukan sada zumunta.

A gefe guda kuma tuni Dagacin Nata’ala ya Kara gurfana a gaban kotu game da zargin da akai ke masa na hada baki da barayi da yan bindiga a yankin wanda ko a jiya Dagacin ya gurfana a gaban hukumomin tsaro domin Kai shi kotu.

To al’umma sai kuyi adalci a nan waye me gaskiya tsakanin hakimi da wadannan mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *