May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kai wa tawagar Atiku Abubakar hari a Maiduguri

2 min read

An kai wa tawagar Atiku Abubakar hari a Maiduguri

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya na cewa wasu matasa sun kai wa jerin-gwanon motocin ɗan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar hari.

An kai harin ne a lokacin da motocin ke kan hanya zuwa dandalin taro na Ramat Square da ke birnin na Maiduguri, domin yi wa magoya bayansa jawabi.

Farmakin ya yi sanadiyyar farfasa wasu motocin da ke cikin jerin gwanon, haka nan wasu bayanai na cewa akwai mutane da aka raunata.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga motoci da dama na yaƙin neman zaɓen Atikun waɗanda aka fasa gilasan su.

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta yi Allah wadai da harin da ta ce wasu ɓata garin siyasa ne suka kai mata a yayin yaƙin neman zaben da take yi a birnin Maidugurin.

PDP ta ɗora alhakin wannan hari kan gwamnatin APC Jihar Bornon.

Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutum 70 aka raunata a yayin harin sa’nnan baya ga motoci da aka lalata da ƴan jam’iyyar.

Ladan Salihu wanda Jigo ne a Jam’iyyar PDP kuma yana ɗaya daga cikin kwambar motocin da aka kai wa harin ya mana ƙarin bayani kan yadda lamarin ya kasance.

Sai dai a nata bangaren gwamnatin Jihar Borno ta bakin kakakinta Isa Gusau, ta musanta zargin da PDP’n ke yi mata inda hasali ma ta ce watakila PDP’n ce ta shirya harin.

Hare-hare kan ayari ko kwambar motocin yakin neman zabe musamman idan an kada gangar siyasa ba sabon abu bane a Najeriya inda aka sha tafka asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon wannan lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *