July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Malaman jami’a za su tsunduma yajin aiki a Birtaniya

1 min read

Malaman jami’a a faɗin Birtaniya za su fara yajin aiki a wannan watan kan taƙaddamar albashi, da fansho da kuma yanayin aiki, in ji kungiyar jami’a ta kasar UCU.

Za a yi yajin aikin ne a ranakun 24, 25 da 30 ga watan Nuwamba a jami’o’i 150.

Ƙungiyar malaman jami’o’in ta UCU ta ce kimanin malamai 70,000 ne ake sa ran za su shiga yajin aiki, ko da yake ta yi tanadi domin ganin hakan bai shafi karatun ɗalibai ba.

Lamarin ya samo asali ne kan amfani da tsarin biyan malamai ta asusun ƴan fansho da aka shafe shekaru goma ana taƙaddama a kai.

Ƙungiyar malaman jami’oin ta UCU na son a yi ƙarin albashi da zai yi daidai da yadda ake samun ƙaruwar farashi, kamar yadda sauran kungiyoyoyin ma’aikata na wasu ɓangarori suke ta hanƙoro a watannin baya bayan nan.

Ƙaruwar farashin da ake fama da ita a Burtaniya ita ce mafi muni da aka gani a tsawon shekaru 40.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *