May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dambarwa ta barke a jam’iyyar PDP a jihar Yobe

2 min read

Har yanzu tana kasa tana dabo, dangane da batun takamaiman dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a jam’iyyar PDP ta mazabar Gujba da Gulani da Damataru da kuma Tarmasuwa a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan ja-in-jar da ake yi tsakanin Abdullahi Idris, wanda ya ce shi ne sahihin dan takarar wannan kujerar da aka zaba ba tare da hamayya ba, da kuma wasu shugabannin reshen jam’iyyar PDP a jihar ta Yobe, da suka ce wannan dan takara shi ya janye takarar tasa, saboda haka ake kokarin maye gurbinsa da wani.

Duk wannan dambarwa, har yanzu dan takarar kujerar na farko Abdullahi Idiris, na nan a kan bakansa cewa shi ne dan takarar wannan kujera.

Abdullahi Idris ya shaida wa BBC cewa shi ne cikakken dan takarar da ya sayi tikitin takara ya cike, kana kuma shi ne mutumin da aka tantance a matsayin dan takara.

Ya ce “Ni ne kuma mutumin da aka bai wa takardar cewa ni ne na ci zaben fitar da gwani wanda kuma babu abokin hamayya, sannan ni ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tabbatar a matsayin halattaccen dan takara.”

Abdullahi Idris, ya ce a don haka a halin da ake ciki a yanzu ya garzaya kotu inda a karshe ma har kotu ta bashi takararsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *