May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Darajar Naira ta fara farfaɗowa a kasuwa – Za ta ɗore ko kuwa?

2 min read

Darajar kuɗin Najeriya ta naira ta ɗan farfaɗo da kashi 16.3 cikin 100 a kwana uku idan aka kwatanta da faɗuwar da ta dinga yi da kashi 36.52 cikin 100 a shekarar 2022.

Ɗan kasuwar canji a Kano, Sani Dada, ya faɗa wa BBC Hausa cewa kasuwar canji ta bayan-fage ta tashi a ranar Alhamis ana canzar da dalar Amurka ɗaya tsakanin N750 zuwa N760 a Kano.

A makon da ya gabata, an canzar da dala ɗaya kan N890 a kasuwar da ba ta hukuma ba, yayin da farashin bai wuce N439 ba a farashin gwamnati.

Sai dai ana danganta farfaɗowar nairar da ƙarancinta da aka fara fuskanta a kasuwar canjin sakamakon wa’adin da CBN ya bayar na soke amfani da tsofaffin takardun naira na N200 da N500 da N1,000 na ƙaratowa.

Cikin matakan da CBN zai iya ɗauka akwai ƙara yawan dalar da yake bai wa bankuna a kullum, wanda hakan zai rage yawan nemanta da ‘yan kasuwa da ɗaiɗaikun mutane ke yi.

Ranar 31 ga Janairun 2023 ne CBN ya bayar a matsayin wa’adin da tsofaffin kuɗaɗen za su daina aiki, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne saboda rage yawan garin kuɗi a hannun mutane da kuma daƙile masu buga jabun kuɗi.

A cewar CBN, matakin zai taimaka wajen rage hauhawar farashi a faɗin ƙasa, ƙari a kan sauran matakai na ƙara yawan kuɗin ruwa.

Haka abin yake a Legas da Abuja da Fatakwal
Naira
ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Rahotanni sun nuna cewa darajar nairar ta samu tagomashi har a sauran manyan birane kamar Legas da Abuja da Fatakwal – babban birnin Jihar Ribas.

Saboda yadda lamarin ke sauyawa cikin sauri da kuma rashin tabbas, babu wani takamaiman farashin da aka canzar da dalar a Legas a ranar Alhamis.

An canzar da dala kan N700 har zuwa N730.

A birnin Fatakwal ma ta sauko zuwa N700 da kuma N720.

‘Yan kasuwar canji a Abuja sun ce tun daga ranar Talata suka fuskanci faɗuwar darajar dalar saboda dalilai daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *