May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wata Gobarar Tsakar Dare Ta Lakume Rayukan Mutane 3 A Kano

2 min read

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku, biyo bayan wata gobara da ta tashi a kasuwar Badume da ke karamar hukumar Bichi a ranar Juma’a.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Kano.

Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta cinye shaguna na wucin gadi 100.

“Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara na Bichi da misalin karfe 03:30 na dare daga wani Ibrahim Tsalha cewa gobara ta tashi a kasuwar kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 03:35 na daren domin hana wutar yaduwa zuwa wasu shaguna.

“Mutanenmu sun kwashe mutane uku da ba su sa hayyacin su, daga baya aka tabbatar sun mutu sannan aka mika gawarwakin ga Sufeto Mukaila Inusa na sashin ‘yan sanda na Bichi.

“Wadanda suka rasun sun hada da mace daya ‘yar kimanin shekara 35, gurgu mai kimanin shekaru 30 da kuma wani matashi dan kimanin shekara 18, har yanzu ba a tabbatar da sunayensu ba,” inji shi.

Bustandaily ta rawaito cewa Abdullahi ya kara da cewa tuni hukumar ta fara gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar.

Ya shawarci jama’a da su kashe duk na’urorin wutar lantarki, a cire su daga inda ba amfani ake da su ba, sannan a kula da wuta. (NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *