May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Martani – Al’ummar Garin Nata’ala sun ce ba ‘yan Garin Nata’ala bane suka yada cewa Dagacin Garin Nata’ala na hada baki da barayi domin satar mutane a yankin

2 min read

Al’ummar Garin Nata’ala dake cikin karamar hukumar Tudun Wada a nan Kano,sun bayyana cewa labarin da Freedom Radio da Express Radio da Premier Radio suka yada a jiya na cewa wasu manoma a karamar hukumar Tudun Wada su yada a jiya akan Dagacin Garin Nata’ala ba gaskiya bane, domin Kuwa mutanan ba ‘yan Garin Nata’ala ba ne.

A jiya Talata ne dai wasu kafafan yada labarai a nan jihar Kano suka bayyana labarin cewa Dagacin Garin Nata’ala na daya daga cikin mutanen da ke hada baki da barayi idan barayi sun sato mutane domin bashi wani kaso daga cikin kudin fansa.

Al’ummar yankin sun bayyana cewa mutanan da suka shiga gidajen radio ne da sunan al’ummar Garin Nata’ala ba ‘yan garin Nata’ala bane wasu mutane suka bada hayo su da nufin batawa Nata’ala suna a kokarin da yake na hana zalintar talakawan yankin daga wasu shugabanni a Tudun Wada.

A cewar guda daga cikin yan kwamitin Garin Nata’ala ya bayyana cewa mutanan da suka je gidajen radio a jiya wasu daga cikin su,an dauko hayar su ne daga wasu jihohi domin batawa Nata’ala sunan masarautar Rano da al’ummar jihar Kano.

Sun kuma Bukaci Sarkin Rano Autan Bawo da ya tabbatar ya dauki mataki kan mutanan dake tada fita a kasar sa.

Haka kuma ya bukaci Gwamnatin jihar Kano data dauki mataki da gaggawa akan wannan lamari.

Shima Aljaji Garba Ahmad Wanda Shi ne shugaban kungiyar Da’awa ya bayyana cewa zasu shigar da Kara a kotu bisa batawa Dagacin Nata’ala suna, inda ya ce,an kira na ta’ala da barawo wanda ke daurewa barayi Gindi suna sace mutane domin neman kudin Fansa.

Kwace Gonakin manoma a yankin Tudun Wada na neman zama ruwan dare Gama duniya a yankin wanda mutanan garin Nata’ala a yanzu ke cewa dole ne su dauki mataki akan azzaliman yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *