May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama ‘ƴan fashi 16’ a Zamfara

1 min read

Ƴansanda a jihar Zamfara ta Najeriya sun ce sun kama mutane 16 da ake tuhuma da zama ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane da sauran jinsin miyagu.

Rundunar ta ce ta samu nasarar yin kamen ne a kokarin da take yi na kawar da ayyukan ta’adanci a jihar.

Mai Magana a yawun rundunar ƴansanda a jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya ce an kama su ne a sassa daban-daban na jihar tsakanin ranakun 11 da kuma 14 na watan Disamba.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kaman har da wasu sanannun ƴan fashin daji wadanda aka kama ta amfani da bayanan sirrin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *