May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yin Addu’a tare da zabar shuganni nagari shi ne hanya ta farko wajen kawo sauki a Nigeria

2 min read

Wani Fitaccen Malamin Addini a kasar nan Sheikh Isma’il Umar Mai diwani ya bukaci al’umma dasu dage wajen gudanar da Addu’o’i tare mika komai ga Allah wanda ta haka ne za’a sami saukin matsalolin rayuwa da al’umma ke fuskanta.

Malamin ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da ya kolawo jihar Kano daga garin Kaduna wanda ya sauka a zawiyar Alhajj Habibu Abubakar dake unguwar Tudun Yola a nan Kano.

Tun da fari malamin ya gudanar da zikirin juma’a tare da gabatar da lacca ga al’umma.

Ya kuma jaddada muhimmacin da zumunci yake dashi inda ya ce Allah na alfahari da masu gudanar da zumunci.

Haka kuma ya bayyana godiyarsa bisa karramawar da akai masa.

Da yake nasa jawabin Sheikh Muhammad Nafi’u Alharazimi ya bayyana kira yayi ga al’umma kan muhimmancin girmama janibin Annabi Muhammad S.A.W wanda shi ne hanya mafi da cewa ga Al’umma.

Alhaji Habibu Abubakar wanda shi ne ke jagorantar zawiyar ya bayyana farin cikin sa bisa wannan ziyara,inda ya ce dama chan iyayensu sun ginu ne akan irin wadannan ayyuka da wanda ya ce abune mai matukar fa’ida.

Ya kuma ce za su cigaba da jaddada wannan zumunci domin Allah ne yayi umarni dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *