May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Har yanzu Masu fada-a-ji ‘yan Arewa a soshiyal midiya sun dakatar da tallata Tinubu

2 min read

Wata sabuwar ɓaraka ta kunno-kai tsakanin magoya bayan ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, bayan wata kungiyar ƴan APC ma’abota dandalin sada zumunta daga arewacin kasar ta ce ta janye daga tafiyar.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan matakin ne bayan ta fahimci cewa take-taken ɗan takarar na nuna cewa ba ya bukatar ƴaƴan nata.

Sai dai kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubun ya ce zai duba lamarin.

Magoya bayan jam’iyyar ta APC da kuma ɗan takarar shugaban kasar nata da ke karkashin kungiyar mai suna Arewa APC Media Influencers da Ingilishi sun ce sun dau wannan mataki ne bayan sun fahimci cewa ana yi musu riƙon sakainar-kashi.

A cewar su sun yi wa shugaban kasa mai barin gado makauniyar soyayya, inda aka ci yaƙi da su, amma daga karshe aka mai da su karan kada miya.

Matasan na cewa sun koyi darasi ba za su yi tafiyar Tinubu ba sai an yi dalla-dalla da su, in ji Mallam Rabi`u Ali Biyora shugaban kungiyar

Sai dai kwamitin yaƙin neman zaben Bola Tinubu ya ce ba halin ɗan takarar ba ne watsi da magoya bayan sa, kuma zai bincika.

A Najeriya kusana ana iya cewa da sannu tasirin irin wadannan matasa ma’abota dandalin sada zumunta da aka fi sani da ‘yan soshiyal midiya na karuwa sosai a siyasar kasar.

A yanzu dai ta kai ga wadannan mutane na iya iya sanya soso da sabulu wanke fari ya yi sol, kazalika suna iya mai da fari baki idan aka samu akasi wannan ne ya sa wasu `yan siyasar ke cewa fada da su ba riba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *