May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Al’ummar Garin Nata’ala dake Karamar hukumar Tudun Wada sun zargi Malam Isyaku da Abdullahi bisa cinye gonaki shabiyar a yankin

2 min read

Al’ummar Garin Nata’ala dake cikin karamar Hukumar Tudun Wada sun zargi Wani Mai suna Malam Isyaku da Abdullahi Dan Chabe da karbe musu Gonaki da sunan Hakimin Tudun Wada ne ya aiko su.

A cewar mutanan Malam Isyaku da Danchabe kanzo musu da cewa wadannan Gonakin ba nasu ba ne a dan haka sai dai su sake saya ko a sayarwa da wani mai bukata.

Wasu daga cikin mutanan da lamarin ya shafa sun bayyana cewa Malam Isyaku da Abdullahi dan chabe sun karbri Kudi wasu dubu 300 wasu 500 inda wasu kuma 250.

Mutanan wanda adadin su ya kai kusan kimanin 15 sun ce, Basu da wata Sana’a data wuce Noma, wanda itama gashi ana nema a ra basu da ita.

Abdullahi Danchabe guda ne daga cikin mutanan da ake zargi da karbe gonakin mutane tare da karbar kudade da sunan hakimin a zantawar mu dasu yayi Karin haske game lamarin.

Duk kokarin da mukai naji daga bakin Malam Isyaku wanda Shi ne mutum na farko da mutanan suka ambata bai yadda mun yi magana dashi kusan Karo biyu.

A hakan ne kuma ya sanya muka tuntubi sakataren Hakimin na Tudun Wada Malam Lamido Muhammad Domin ji daga bangaren hakimin inda Sakataren ke ya bayyana cewa wannan magana haka ba haka take ba, domin hakimi bai san wannan magana ta sayar da gonaki ba, a dan haka dai ka mata yayi na koma gurin wancan mutum mai suna Malam Isyaka domin a nan ne zan sami baya bayani mai kyau

Al’ummar da abin ya shafa sun bukaci hukumomi dasu sanya baki domin karbar musu hakkinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *