May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar jindadin Alhazai ta jihar Kano ta fara baiwa Maniyyatan aikin Hajjin da basu sami halartar aikin hajjin da ya gabata ba kudadensu -Alhaji Muhd Abba Dambatta

1 min read

Hukumar jindadin Alhazai ta jihar Kano ta ce daga Ranar Litinin zata fara baiwa Maniyyatan da basu sami halartar da aikin Hajjin daya gabata ba.

Babban Sakataren hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Kano Sarkin Noman Dambatta, Alhaji Muhammad Abba Dambatta ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai da ya gudana a hukumar.

Malam Muhammad Abba Dambatta ya kuma sanar da karbar Naira Miliyan daya da dubu Dari biyar a matsayin wani bangare daga cikin kudin aikin hajjin bana kafin hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta Kasa Nahcon ta sanar da kudin kujerar a bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *