May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Tallafawa Marayu da zaurawa dake Medile da hadin gwiwar Nurul yakim sun raba kayan abinci da iyayen marayu da zaurawa 5OO

1 min read

Kungiyar dake unguwar Medile ta ce ta raba kayan abinci ne domin ragewa marayu da zaurawa radadin tsananin rayuwa da suke fuskanta.

Shugaban kungiyar Kwamared Usman Dalhatu ne ya bayyana haka a yayin taron rabon tallafin da ya gudana a unguwar ta Medile.

Ya Kara da cewa kayan dai an sa mesu ne ta hanyar hadin gwiwa, a kokarin kungiyar naganin marayu sun sami walwala kamar sauran al-umma suke.

A cewar Shugaban abincin da aka raba ya tasarwa sama da naira miliyan biyar.

Wasu daga cikin Marayu da zaurawan da suka amfana da tallafin abincin sun bayyana godiyar su ga Allah bisa wannan taimako da akai musu.

Sun kuma bukaci sauran masu hannu da shuni dasu tallafawa marayu da marasa galihu dake cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *