May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 7 Sun Mutu, 16 Sun Jikkata A Hatsari Ranar Sabuwar Shekara

1 min read

Akalla mutum bakwai sun mutu, wasu 16 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Ranar bikin Sabuwar Shekara a babbar Hanyar Legas-Ibadan.

Hatsarin ya ritsa ne da wata bas kirar Toyota Hiace da kuma tankar mai.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) na Jihar Ogun, Ahmed Umar, shi ne ya tabbatar wa manema labarai aukuwar iftila’in a Abeokuta, babban birnin jihar.

Umar ya ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4:10 na yamma sakamakon gudun wuce hankali daga na direban bas din.

A cewarsa, hakan ne ya sa bas din ta kwace wa direban inda ta daki tankar ta baya.

Ya kara da cewa, baki daya mutum 25 (maza da mata) hatsarin ya shafa inda mutum bakwai suka riga mu Gidan Gaskiya sannan 16 suka jikkata.

(NAN).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *