May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima, ta bayyana babban burin da take da shi game da ƴar ta Surayya Salisu Yahaya

1 min read

Jaruma Hadiza ta bayyana cewa babban burinta ga Surayya shine ta ga ta samu miji nagari domin raya sunnar Annabi Muhammad (SAW), inda tayi addu’ar Allah ya kawo miji nagari ga Surayya.

Hadiza ta yi wannan addu’ar ne a wata hira da Mujallar Fim kan bikin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar Surayya da aka yi a birnin Kano.

An dai gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu 2023.

Lallai babu abin da zan ce da Allah sai godiya da ya nuna mani wannan rana domin wannan abin farin ciki ne a gare ni.”

“A yanzu babban burin da na ke fata shi ne Allah ya nuna mani lokacin auren ta. Ina fatan Allah ya ba ta miji nagari, kuma Allah ya ƙara mana shekaru masu albarka cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.” A cewar ta.

Ƴan fim da dama sun ɗora zafafan hotunan da Surayya tayi a shafukan su na sada zumunta domin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *