July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Daga watan Yuni mun daina biyan tallafin fetur – Gwamnatin Najeriya

1 min read

Gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayarta cewa za ta dakatar da biyan kuin tallafin man fetur nan da ƙarshen watan Yuni mai zuwa.

Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta faɗa yayin gabatar da tanadin kasafin kuɗi na 2023 ranar Laraba cewa gwamnati ta ware naira tiriliyan 3.36 ne kawai don biyan tallafin a wata shidan farko na sabuwar shekara.

A cewarta, matakin ya yi daidai da sanarwar da aka bayar tun a 2022 ta ƙarin wa’adin cire tallafin zuwa wata 18.

Da take fayyace ƙunshin kasafin kuɗin, ministar ta ce kuɗin shigar da Najeriya ta samu zuwa Nuwamban 2022 sun kai naira tiriliyan 6.5, abin da ke nufin ƙasar ta samu ƙarin kashi 87 cikin 100 na hasashen abin da za ta samu a shekarar.

Cikin kuɗaɗen da aka tara sun ƙunshi wanda gwamnatin tarayya ta tara na biliyan N586, hukumar kwastam ta karɓi naira biliyan 15, cibiyoyin karɓar haraji masu zaman kansu sun tara tiriliyan 1.3, sai kuma sauran sashe-sashe da suka tara tiriliyan 3.7.

Gwamnatin Buhari ta APC za ta sauka daga mulki a ƙarshen watan Mayu mai zuwa kuma ɗan takararta na shugaban ƙasa, Bola Tinubu, shi ma ya ce zai cire tallafin idan ya yi nasara a babban zaɓen 2023 “duk irin zanga-zangar da ‘yan ƙasa za su yi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *