May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

2 min read

Hukumomi a Najeriya sun kammala shirin miƙa wasu mayaƙan Boko Haram fiye da 600 da suka tuba ga gwamnatocin jihohinsu domin shigar da su cikin sauran al`umma.

Hedikwatar tsaron Najeriyar ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne bayan an shigar da su cikin wani shirin gyara hali.

Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya bayyana cewa an kammala shirin miƙa mayakan Boko Haram ɗin da suka tuba su 613, bayan an gyara musu hali.

Ya yi bayanin ne a wajen wani taron masu hannu ko ruwa da tsaki a ƙarƙashin tsarin nan na ba da damar miƙa wuya ko tuba ga mayaƙan Boko Haram, wato Operation Safe Corridor.

Ya ce za a mika su ne ga jihohinsu na asali domin shigar da su cikin al`umma, kuma a halin da ake ciki ana gab da kammala aikin sauya musu tunani da zare musu tsattsaurar akida.

A cewar Hafsan hafsoshin, tubabbun mayakan Boko Haram ɗin na bukatar kulawa sosai a wannan gaɓa ta gyara hali da sake shiga cikin jama`a, don haka sai jihohin sun tsaya sosai a kan su.

Batun gyara hali aikin ne jawur, saboda ko a nasu matakin sai da suka haɗa da kwararru daga fannoni daban-daban, da ma’aikatu da hukumomin gwamnati masu yawa, da kuma taimakon kungiyoyin agaji na kasa da kasa.

Ya ce za yi nasarar shigar da tsoffin mayakan cikin al’umma idan jihohi suka yi tsari mai kyau, tare da haɗa gwiwa da sarakunan gargajiya wajen sa-ido a kan tubabbun yayin da suke sajewa a cikin al’umma.

Janar Irabor ya ce idan aka zo sallama ko yaye tsoffin ƴan Boko Haram din, za a ba su guzurin kayan abinci da kayan zaman gida da kuma kayan aiki irin sana’ar da suka koya don fuskantar gangariyar rayuwa.

Game da yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram kuwa, Hafsan hafsoshin ya ce askarawan gwamnati na samuN nasara a kan su, kuma da dama sai mika wuya suke yi sakamakon mamayar dajin Sambisa da zaratan sojojin suka yi da fatattakar su da ake yi inda ta kai ga fiye da mayakan Boko Haram da iyalansu 80,000 sun mika wuya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *