May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A karshe dai -Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya yi sabon Aure

1 min read

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya auri mata ta biyu Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko a Kano ranar Juma’a.

Jaridar bustandaily ta rawaito cewa an gudanar da daurin auren ne a gidan marigayi Jarman Kano Farfesa Isah Hashim da ke unguwar Nasarawa GRA a cikin babban birnin tarayya.

Sannan kuma Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim ne ya wakilci Mai Martaba Sarkin a lokacin daurin auren, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya kasance waliyin amarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *