May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A watan Janairu zamu tabbatar an gyara titunan tungaYamadawa Kuntau – Lawan Ken-Ken

2 min read

Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Gwale Alhaji Lawan Kenken yace gwamnatin tarayya zata fara gudanar da aikin titin Tunga/Yamadawa/Kuntau a cikin watan janairun shekarar nan da muke ciki da yardar Allah.

Alhaji Lawan Kenken ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da jaridar time express a Kano.

Yace zaayi aikin titin ne karkashin aikin magance zaizayar kasa wanda gwamnatin tarayya ke gudanarwa.

“Ba zama muke ba a matsayin mu na yan majalisu, mukan bibiyi maaikatu da hukumomin gwamnati da maaikatu don samowa alummar da muke wakilta ayyukan da za su amfana da romon dimokraddiya”

Duk wasu matakai da shirye shirye don fara gudanar da aikin titin sun kammala ,kuma insha Allah cikin watan janairun nan da muke ciki alummar wannan yankin zasu ga anzo an fara wannan aikin”

Alhaji Lawan Kenken yace ya gudanar da irin wannan aikin a titin unguwar bello da ke dorayi wanda tuni an kammala har alumma sun fara amfana, munyi musu titi na zamani da kwalbatoci,ina farin ciki da wannan aikin titin domin kuwa rayuwar alummar yankin ta inganta.

Danmajalisar tarayyar wanda ya samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana sama da 60 yace ba zai taba gajiyawa ba wajen cigaba ya yiwa alummar da suka tura wakilci hidima don su cigaba da kwankwadan romon dimokraddiya.

Alhaji Lawan Kenken yace daga lokacin da alummar karamar hukumar Gwale suka tura shi wakilci a majalisar tarayya , ya samawa matasan karamar hukumar aikin damara, wastau soja,dan sanda, civil defence da makamantansu sama da dari da Hamsin.

“Akwai akin titin kofar waika , muna nan muna bakin kokari wajen ganin shi ma an gudanar da shi da yardar Allah, don haka muna so ku cigaba da bamu goyon baya don mu samu nasara a zabubbukan da ke tafe saboda mu dora daga inda muke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *