May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bayan barkewar rikici a masallacin Dakta Ahmad wanda ya haifar da Hana gudanar da sallar Juma’a a jiya shi kuwa Kwamitin kula da Tafsir Marigayi Sheikh Aisami sun tabbatar da Malam Nura Adamu a matsayin wanda zai gudanar da Tafsir a matsayin Magajin Malam

1 min read

MALAM NURA ADAMU SHI ZAIYI TAFSIR A MADADIN SHEIKH GONI GONI AISAMI: Sheikh Goni Aisami Nurul islam Foundation Ta cimma matsaya Akan wanda zasu cigabada da jagorantar Harkokin Waazin yasheikh Inda Ta Ayyana Sheikh Muhammmad Nura Adam Shi zaiyi Tafsir Na Ramadan Kamar yadda Malam Yasaba.

Sheikh Nura Almajirin Yasheikh Ne Tin Tali Tali Awajen malam yayi karatu Kuma insha Allah Muna Da kyakkyawar Niyan Malam Nura Zai daura Daga Inda Malam Yatsaya. Inda Aka Ayyana Malam Sani zango A matsayin Shugaban Majalissar Malamai inda zaina jagorantar duk abubuwan dasuka shafi malamai A Nurul Islam kamar jagorantar sallan gawa,Jagorantar daurin Aure, Karatun Fikhu,dasauran ayyukan malumta Na yau da kullum. Ustaz Sadik Alh Kyari Zai Cigaba Da Amsa Fatawa A zaurukan Sheikh Goni Aisami Guda biyar. Malam isa Ibrahim Tsohon limamin kofar halliru zaiyi Karatun hadisi A majalisin malam. Malam Abbas Shugaban Alarammomi wanda Malam lukman zai zama mataimakinsa. SIGNED DIR PRESS MEDIA AND PUBLICITY NURUL ISLAM( YUNUS BOSKA)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *