May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sama da al’umma Dubu Talatin dake yankin Sabon Garin Gadan dake cikin karamar Hukumar Ungoggo ne suka yi barazanar kauracewa zaben 2023 a sakamakon matsalolin da suke fuskanta batare da kawo dauki daga bangaren ‘yan siyasa da Gwamnati ba

2 min read

Mataimakin Shugaban kungiyar Cigaban Garin Gadan Alhaji Garba Ibrahim Gadan ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya a yankin.

Shugaban ya ce yankin nasu na fama da matsalar hanya tsahon shekaru batare da samun Wani tallafi daga gwamnati ba, wanda suke ganin a yanzu ba za su sake bari a kawo akwatinan zabe yankin nasu ba, da sunan zabe.

Shugaban ya kuma Kara da cewa Yan majalisar tarayya dana majalisar jihar masu wakiltar yankin basu amfanar dasu komai ba, a dan haka lokaci yayi da al’ummar yankin zasu yi watsi dasu Baki daya.
Al’ummar yankin sun kuma ce hatta makarantun islamiyya dana Boko Garin Gadan basu dashi, sai dai Makaranta daya da ‘ya’yansu Mata da Maza suke amfani da ita a takure, wacce itama Marigayi Na Baba Badamasi ne ya Gina musu ce.

Da yake nasa jawabin Alhaji Muhammad Rabi’u Mai iyali shugaban Kwamitin Matasan Cigaban Sabon Garin Gadan Ya ce, Sabon Garin Gadan basu da wutar Lantarki a yankin, tun bayan lalacewa da wutar tayi tsahon shekaru batare da kawo dauki daga hukumomin da abin ya shafa ba.

Ya kuma ce sun Kai kukansu a rubuce ga bangarori da da ban da bam batare da kawo wani dauki ba.

Ya kuma ce, akwai ‘Yan siyasar da da su ka yi masu alkawarin kawo wutar Lantarki a yankin, wanda har sun turo da wakilai sun duba inda za’a saka na’urar wutar Lantarkin amma shiru kake ji wai Malam ya ci shirwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *