May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An tsaurara binciken kuɓutar da fasinjoji 32 da aka yi garkuwa da su a tashar jirgin Edo

1 min read

Sojoji da ‘yan sanda da jami’an vigilante na ci gaba da lalube domin kuɓutar da fasinjoji 32 da aka yi garkuwa da su a tashar jirgin ƙasa ta garin Igueben da ke Edo.

Cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai mai kula da tashar, Godwin Okpe da shugaban jami’an tsaro, da aka bayyana sunansa da Ikhayere da fasinjoji 29.

‘Yan sanda dai sun ce suna iya kokarin su domin kuɓutar da fasinjoji.

Wannan hari na zuwa ne watanni 10 bayan kazamin harin ‘yan bindiga kan jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna, mutum 14 suka mutu sannan aka yi garkuwa da 65.

An saki fasinjoji bayan shafe watanni da biyan kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *