July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Matar shugaban SSS ta umarci jami’ai su kama Abba Kabir, kuma su hallaka guda cikin hadimansa

2 min read

Aisha Bichi, wacce mata ce ga shugaban hukumar tsaron farin kaya (SSS), Yusuf Bichi, tayi umarnin a kama dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) domin hana shi hawa jirgin Max Air daga Kano zuwa Abuja a daren ranar Lahadi, sakamakon tsaiko da tawagar Abba ta janyo a filin sauka da jiragen sama na Malam Aminu Kano dake Kano.

Wani Rahoto da jaridar Daily Nigerian ta fitar, ya bayyana cewa, tsaikon ya bata ran ita Aisha, lamarin da yasa jami’anta suka fara dukan mutane da ababen hawa bisa rashin girmama Madam, har sai da shi Abba ya shiga dakin jira ya same ta tare da korafi bisa abinda jami’an tsaro suka aikata ga mutanensa.

Wata majiya ta bayyana cewa, yayin da Abba ke mata bayani, sai ta fara fadar maganganu marasa dadi akansa, dukda wani babban jami’i na bata hakuri, amma ta cigaba har tana mai cewa, ba zata bari Abba ya zama gwamnan jihar Kano ba, kamar yadda majiyar ta bayyana.

Lamarin ya ƙara zafi ne yayin da ta ga wani hadimin Abba mai suna Garba Kilo yana daukar bidiyo a wayarsa, nan ta ke ta umarci jami’ai su hallaka shi kuma ba abinda zai faru.

Madam Aisha ta turje akan cewa ba zata hau jirgi guda da Abba ba, wanda a karshe DPO na yan sanda dake filin jirgin ya hallara, tare da karɓar bayanai daga bangaren shi Abba akan lamarin da ya faru.

Amma bisa mamaki, yayin da DPO ya koma ga bangaren Madam Aisha domin karbar bayanai, sai bata bashi bayanin komai ba, tana mai cewa, “ka san ni wacece? Waye kai da zaka zo kana cewa na rubuta bayanai?” Haka DPO ya tafi ba tare da karɓar bayanai daga bangaren ta ba, kamar yadda majiyar ta bayyana.

Ana zargin Madam Aisha da amfani da jama’ai a wasu al’amura nata, domin ko kwanakin baya an zarge ta da bada umarnin dukan wani mai yi mata dinki (Tela) a Abuja, sakamakon rashin kammala mata aiki akan lokaci.

Har kawo yanzu dukkan bangarorin guda biyu basu ce komai akan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *