May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tawagar Nijeriya da ta isa Saudiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU), tare da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Masarautar dangane da aikin Hajjin 2023

1 min read

Tawagar Nijeriya da ta isa Saudiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU), tare da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Masarautar dangane da aikin Hajjin 2023.

A wata sanarwa da shugaban yada labarai na hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Mousa Ubandawaki ya fitar a jiya Lahadi, ta ce tawagar Najeriyar ta na karkashin jagorancin karamin ministan harkokin wajen kasar, Zubair Dada l.

Ubandawaki ya ce tawagar ta kuma hada da, Sanata Adamu Bulkachuwa, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kasashen waje, Abubakar Nalaraba, shugaban kwamitin majalissar kan aikin hajji, shugaba/shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, da kuma wasu daga cikin mambobin hukumar da ma’aikatan NAHCON.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *