May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Me yasa ake cigaba da samun laifukan kisan Kai ne a Jihar Kano.?

2 min read

Daga Abubakar Sale Yakub.

Bisa zargi Mai karfi Ace matashi Dan shekara 20, dan ka wai ya samu sabani da matar mahaifinsa ya dauki makami ya halakata tare da Yarta kai wannan rashin Imani ya munana.

Gaskiya laifukan kisan kai suna karuwa a sassan Jihar Kano, la’akari da yadda abin yake cigaba tun a shekarar data gaba ta 2022, domin a shekarar sai da wani Yaro me matsakaicin shekaru ya halaka Yar uwar mahaifiyarsa dan kawai ya sace wayarta ya bugamata Tabarya.

Kazalika a shekarar wasu Yan fashin waya da makami suka halaka wani magidanci a kan titin Yahaya Gusau, haka wasu suka halaka wani Yaro a kusa da cibiyar Abacha Youth Center dake hanyar Madobi, ga Hanifa Yarinya Karama da Malaminta ya kasheta.

Shin me yasa bayan an kammala shari’a ba iya aiwatar da hukunci akan wadanda aka samu da laifin kashe wani ko wata?

Me yasa kungiyoyin kare hakkin Dan Adam basa iya magana wajen tabbatar da hukuncin kisa kan mutanen da aka samu da laifin kisa?

Shin me yasa Malamai suka fi mayar da hankali kan lamarin Duniya a yanzu Mai makon fadakar da mutane illar aikata laifin kisan kai.?

Me yasa Shugaban dake da ikon tabbatar da hukuncin kisa kan mutanen da aka samu da laifin kashe wani ko wata ba a Sanya hannu wajen aiwatar da hukuncin?.

‘Ƴansanda suna bakin kokari la’akari da yadda sukan kama tare da bincike da Kuma gabatarwa gaban kotu.

Kazalika akwai zargi Mai karfi na cewa fina finai da ake haskawa a shafukan YouTube da Facebook da sauran Shafuka suna nunawa Yara yadda ake sarrafa makami da sanin makasa a jikin Dan Adam, ayi dubayya akansu.

Irin wadannan fina finai da aka kwafosu daga Indiya suna taka rawa wajen cusawa Yara masu kananan shekaru rashin Imani da sanin makasa a jikin Dan Adam.


Shin Ina Hukumar tace fina finai ta Jihar Kano, data Najeriya? domin za a iya zargin cewa basa iya ko mai sabo da tara kudaden shigar su, a iya cewa sai dai daukar matakin yakan so akan wadanda suka soki abin da suke karewa wato Gwamnati.

Iyaye ya zama wajibi ku farka ku rika zama tare da yin hira da ‘ya yan ku, domin barin su sakaka shike baiwa wasu damar sarrafasu yadda suke so.

Sannan kusan da suwa suke yawo, a kuma cigaba da yi musu addu’a adaina La’antarsu.

Gyara kayanka bai taba zama sauke mu raba ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *