May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za mu tabbatar babu sunayen bogi cikin sabuwar rajistar zabe’

2 min read

Jam’iyyu a Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu tun bayan gabatar musu da kundin rijistar masu zaɓe da Hukumar zabe ta kasar, INEC ta yi a ranar Laraba.

Cikin adadin masu zaɓe sama da miliyan 93 da kundin rijistar ya ƙunsa, maza ne suka fi yawa inda suka kai sama da miliyan 49, sai mata su kuma sama da miliyan 44.

Injiniya Yabagi Sani shi ne shugaban kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyu wato IPAC.

Ya ce dokar zabe ta kasa ta tilastawa hukumar zaben ta mika wa dukkan jam’iyyun siyasa na kasar kundin rajistar masu zaben da ta hada.

“Wannan zai ba jam’iyyu damar sanin inda wadanda aka yi wa rajista suke, da inda za a same su.

Kan haka ne jam’iyyun za su iya sanin adadin wadanda suka yi rajistar da inda za iya samunsu.”

Ya ce bayan sun karbi rajistar zaben, jam’iyyun siyasar za su gudanar da bincike kan wadanda ke da katin zabe wato PVC da ‘yan jam’iyyar da ba su da katin samsam.

A Nigerian woman getting verified to vote
ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Kan ko jam’iyyun siyasar sun gamsu da kundin masu rajistar, Injinaya Yabagi ya ce a baya akwai damuwa cewa rajistar zaben ta kunshi sunayen wasu mutane na bogi, amma bayan an gudanar da bincike mai zurfi, an gano ba haka lamarin yake ba.

“Wannan duka babu kurakurai yanzu. In dai Allah yasa INEC ta yi aiki da wannan rajistar kamar yadda aka tsara, da kuma yadda suka yi alakawarin yi, to ina ganin zai kawo wani sauyi mai ma’ana.”

Ya yi kira ga hukumar zaben da ma jam’iyyun siyasa na Najeriya, da su tashi tsaye wajen wayar da kawunan al’ummar kasar.

“Ya kamata mu sami jama’a domin mu tabbatar sun karbi katunan zabensu daga hukumar zabe, domin wannan zai ba mu damar tabbatar da sunayen da aka wallafa a kundin zaben masu sahihanci ne, ba cushe aka yi ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *