May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Da dumi-dumi: Gobara ta tashi a hedikwatar ‘yan sandan jihar Kano

1 min read

Hedkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai a karamar hukumar Nasarawa, tana cin wuta, inda ake zargin ta kona ofisoshi da muhimman bayanai da dama. Be

Da dumi-dumi: Gobara ta tashi a hedikwatar ‘yan sandan jihar Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce tuni ta tura jami’an ta wurin da lamarin ya faru domin dakile gobarar da ta tashi a ginin bene mai hawa daya na rundunar.

Rahotanni da basu tabbata ba sun nuna cewa gobara ta tashi ne a saman benen, Inda ta kama ko’ina amma banda ofishin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda.

Ko da tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar hannu, mun sami wayarsa a kashe har lokacin haɗa wannan rahoton, amma har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *