July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da Kamfanonin Jigilar Alhazai na Jirgin Yawo sun yi alkawarin karfafa aiki Kafada da Kafada domin hidimtawa Maniyyata Kasar nan aikin Hajji bana

3 min read

A cikin takardar da aka rabawa manema labarai wadda mataimakin daraktan yada labarai na Hukumar ta NAHCON Musa Uban Dawaki ya sanyawa hannu, ta bayyana cewar Hukumar aikin hajji ta kasa (NAHCON) tayi wannan taron tattaunawar ne a mabambamtan lokuta tare da Shugabannin Hukumomin Alhazan Jihohi da Kuma Wakilan Shugabannin Kamfanonin Jigilar Maniyyata Aikin Hajji da Umra ta Jirgin Yawo a babban ofishin Hukumar ta NAHCON da ke Ummul Jud a birnin Makka.

Taron tattaunawar dai ya sami halartar Shugaban Hukumar Alhaji Zilkirullahi Kunle Hasan da Kwamishinan Gudanarwa da harkokin Kudi Alhaji Nura Hasan Yakasai da Kwamishinan Harkokin Jigilar Alhazai Alhaji Magaji Hardawa da Kwamishinan Binciki, tsare tsare da Yada labaru Sheikh Suleiman Momoh da Wakilan Hukumar Daraktocin Hukumar aikin Hajji ta Kasa.

Pyramid FM Kano – Hausa

ADDINI
2 minute read
HAJJI 2023: NAHCON Da Hukumomin Jindadin Alhazai Na Jihohi Da Kamfanonin Jiragen Sama Sunyi Alkawarin Aiki Tare.

Sani Magaji Garko
January 15, 2023

Daga: Abba Bashir

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da Kamfanonin Jigilar Alhazai na Jirgin Yawo sun yi alkawarin karfafa aiki Kafada da Kafada domin hidimtawa Maniyyata Kasar nan a aikin Hajji bana.

A cikin takardar da aka rabawa manema labarai wadda mataimakin daraktan yada labarai na Hukumar ta NAHCON Musa Uban Dawaki ya sanyawa hannu, ta bayyana cewar Hukumar aikin hajji ta kasa (NAHCON) tayi wannan taron tattaunawar ne a mabambamtan lokuta tare da Shugabannin Hukumomin Alhazan Jihohi da Kuma Wakilan Shugabannin Kamfanonin Jigilar Maniyyata Aikin Hajji da Umra ta Jirgin Yawo a babban ofishin Hukumar ta NAHCON da ke Ummul Jud a birnin Makka.

Taron tattaunawar dai ya sami halartar Shugaban Hukumar Alhaji Zilkirullahi Kunle Hasan da Kwamishinan Gudanarwa da harkokin Kudi Alhaji Nura Hasan Yakasai da Kwamishinan Harkokin Jigilar Alhazai Alhaji Magaji Hardawa da Kwamishinan Binciki, tsare tsare da Yada labaru Sheikh Suleiman Momoh da Wakilan Hukumar Daraktocin Hukumar aikin Hajji ta Kasa.

Ku Karanta: Mun Shirya Ceto Kano, Inganta Kasuwanci Da Gina Al’umma Idan Mukayi Nasarar Cin Zabe — Tanko Yakasai

Tunda fari Shugaban Hukumar Alhaji Zilkirullahi Kunle Hasan ya bayyana maidawo Kasar nan cikakkun kujerun aikin Hajji dubu 95 a matsayin Wani yunkuri da ya wajabtawa masu Ruwa da tsakin tashi tsaye wajen aiki tare domin cimma nasara.

Shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar Dattijan Kasa, Santa Adamu Bulkachuwa ya bayyana samun bayanan fara Shirin aikin Hajji na bana da wuri daga Hukumomin kasar Saudiyya ya zama kalubale wajen tashi tsaye tare hukumonin Alhazan Jihohi domin kafa tarihin gudanar da Aikin Hajjin bana ya zama Mafi tsari da inganci da aka jima ba a samu ba.

A nasa bangaren karamin Jakadan Kasarnan a Birnin Jeddah Ambassador Mansur Abdulkareem ya bukaci hukumonin Alhazan Jihohi da su tashi tsaye wajen Ilmantarwa tare da wayar da kan Maniyyata Aikin Hajjin na bana domin Samun Hajji karbabbiya.

Sakataren Hukumar Jindadin Alhazan Jigar Niger, Alhaji Umar Makun cewa yayi wannan taron tattaunawar da aka fara da wuri ya nuna hadin kan da ke tsakanin bangarorin uku kuma zai haifar da cikakkiyar nasara a karshen aikin Hajjin na bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *