July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

2 min read

Gwamnatin Najeriya ta ƙara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8 inda a halin yanzu farashin ya koma naira 185 Legas da kuma 220 a wasu sassa.

Shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Jihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa BBC da ƙarin inda ya ce sun samu umarni daga gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa a Legas za a sayar da man fetur ɗin a kan 185 sai kuma a kudu maso yamma kuma 190.

Sa’annan a kudu maso kudu da kudu maso yamma da kuma arewa ta tsakiya za a rinƙa sayar da man fetur ɗin kan 195.

Amma kuma a arewa maso gabas za a rinƙa sayar da man kan 200 sai kuma 220 a arewa maso yamma, kamar yadda Bashir Danmallam ya bayyana.

Sai dai dama tun kafin gwamnatin Najeriya ta yi wannan ƙarin farashin tuni wasu gidajen mai a Najeriya suke sayar da man a farashin da ya fi na hukuma.

Akwai masu sayarwa kan 190 har zuwa 350 a wasu jihohi da ke faɗin ƙasar.

Kafin yin wannan ƙarin, akwai gidajen mai da dama a fadin Najeriya waɗanda ba su iya sayar da mai saboda ƙarancinsa.

Ƙarin farashin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ministar kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed ta tabbatar da cewa akwai yiwuwar a soma cire tallafin man fetur daga watan Afrilu.

Amfani biyar game da samun man fetur a Arewacin Najeriya
23 Nuwamba 2022
Akwai yiwuwar cire tallafin man fetur a ƙasar sakamakon kusan duka ƴan takarar shugabancin Najeriyar sun lashi takobin cire tallafin fetur ɗin inda suka ce ba su ga amfaninsa ba.

Farashin makamashi a Najeriya dai ya yi tashin gwauron zabi ne tun a bara jim kaɗan bayan soma yaƙin Ukraine.

Farashin man dizal wanda ake amfani da shi wurin dakon man fetur sai da ya kai kusan naira dubu a kowace lita, wanda hakan ya sa masu sayar da mai suke kasa zuwa Legas domin su yi dakon fetur ɗin.

Haka ma farashin gas ɗin girki shi ma sai da ya kai har naira dubu goma a duk tukunya mai nauyin kilo 12.5.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *