Masarautar Kano ta Magantu dame da rashin tallafawa Makarantun Islamiyya
1 min read
Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umma musamman masu hannu da shuni dasu dage wajen taimaka Makarantun islamiyya da ke fadin Jihar Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne a yayin taron Bikin saukar Alqur’ani Mai Girma na Makarantar Madrasatul Abiybakar Bn Abiy Quhafa Al-Islamiyya dake unguwar Janbulo.
Sarkin ya kuma bukaci daliban da suka sauke Alqur’ani dasu Cigaba da neman ilimi domin ciyar da al’umma gaba.
A nasa jawabin Shugaban Makarantar Malam Abdullahi Yusuf Maigari, bayyana cewa Makarantar ta samu nasarori da dama a bangarori da dama.
Ya kuma ce Makarantar na fama da matsaloli masu yawa wanda akwai bukatar mawadata dasu kawo tallafi domin Cigaban ilimi a fadin yankin.
Wasu daga cikin daliban da suka sauke Alqur’anin sun bayyana farin cikin su bisa sauke Alqur’anin.