July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

1 min read

Mai unguwar Medile B Alhaji Abubakar Yusuf Ibrahim yayi kira ga al’umma musamman mawadata dasu dage wajen tallafawa Marayu da marasa galihu dake cikin al’umma.

Alhaji Abubakar yayi wannan kiran ne yayin Rabon kayan sanyi ga Wasu Marayu dake yankin.

Mai unguwar ya kuma ce da al’umma zasu dage wajen hada kudade domin tallafawa Marayu da an rage Wasu daga cikin matsalolin da marayun suke ciki.

Da ya ke nasa jawabin Shugaban kungiyar tallafawa Marayu dake unguwar Medile Alhaji Usman Dalhatu, ya ce sun raba kayan sanyi ga gidaje 253, wanda kadan ne daga cikin adadin Marayun da ake dasu a yankin.

Ya kuma bukaci sauran masu hannu da shuni dasu dage wajen tallafawa kungiyar domin Cigaban Marayun.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun bayyana farin cikin su, tare da godewa kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *