May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Alhaji Atiku Abubakar ya karbi Bakwancin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar

1 min read

Dan takarar kujerar Shugaban Kasa a karkashin Inwar Jami’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya karbi Bakwancin Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar a gidansa dake Maitama Abuja.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana farin cikinsa bisa wannan ziyara da Hafiz Abubakar ya kawo masa.

Ya kuma ce, ziyara ta zo a kan gaba musamman a lokacin da Kasar nan take neman ingantattun mutane domin dawo da Kasar nan kan turba.

Ya Kara da cewa irin su Farfesa Hafiz Abubakar sune a ke bukaci domin kawo sauyi mai ma’ana ta fannoni da dama .

A nasa jawabin Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya ce, Kasar nan na bukatar Shugaba mai kishin al’umma wanda zai iya kawo Sauyi da Cigaba ga al’umma.

Ya kuma ce a halin yanzu sun gamsu da salon Alhaji Atiku Abubakar, inda ya bayyana cewa za suyi iya kokarinsu domin ganin Atiku Abubakar ya lashe kujerar Shugaban Nigeria a zaben 2023.

Ya kuma Kara da cewa shi da mutanansa zasu goyawa takarar Atiku, inda ya ce,daga cikin mutanan da yake jagoranta akwai masu ilimi da kwararru a fannoni da dama da matasa Malamai da Mata da dai saurasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *